<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>43</hymn_number>
<title>Yi Addu'a, Ba Fasawa LW43</title>
<lyrics>[V1]
 1) Yi addu'a, ba fasawa,
 Kullayaumin ka yi addu'a.
 Duk ka roƙa Allah ya ji.
 Ba ya ta da alkawari.

[V2]
 2) Yi addu'a, ba fasawa,
 Ba kankanta a idonsa.
 Buɗe zuciya a gabansa,
 Yi addu'a, shi ne mai ji.

[V3]
 3) Yi addu'a, ba fasawa,
 Kada Mugun ya yi nasara.
 Yesu wanda an jarraba
 Zai riƙe ka, ka yi addu'a.

[V4]
 4) Yi addu'a, ba fasawa,
 Ko da ƙunci ya danne ka.
 Ba ya kyale wahalarka,
 Zai daidaita, ka yi addu'a.

[V5]
 5) Yi addu'a, ba fasawa,
 Kwanciyar ranmu sai bangaskiya.
 Allah shi ne mai amsawa,
 Dole kullum mu yi addu'a.</lyrics>
</song>